bbc.co.uk navigation

Dubun- dubatar mutane na tserewa fadan arewacin Mali

An sabunta: 24 ga Fabrairu, 2012 - An wallafa a 06:38 GMT
Sansanin 'yan gudun hijira a Mali

Ana cigaba da samun dubun- dubatar mutanen dake tserewa fadan arewacin Mali

Majalisar dinkin duniya ta ce adadin mutanen da suka guje wa fadan da ake gwabzawa a arewacin Kasar Mali ya haura dubu dari da ashirin.

Kusan dai dukkanin mutanen da su ka tsere sun tsallaka ne zuwa Kasashen makwabta irinsu Mauritania da Nijer da Burkina-Faso.

A watan da ya gabata ne aka fara gwabza fadan a Mali, lokacin da mayakan buzaye suka hada kai da gungun wasu 'yan tawaye, su ka rinka kai hare-hare a garuruwan dake arewacin Kasar da sansanonin soji.

Kawo yanzu dai, babu wata majiya mai zaman kan ta da ta tantance yawan mutanen da aka kashe a fadan.

Kari a kan wannan labari

BBC © 2012 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.