
Taron Kasashen duniya akan rikicin Somalia
Barazana daga ta'addanci da fashin jiragen ruwa na daga cikin abubuwan da za a tattauna a wurin taron da ake yi kan makomar kasar Somalia a birnin Lobndon.
Wakilai daga kasashe 40 ne ke halartar taron, domin bayar da shawara kan yadda za a fuskanci matsalolin da ke addabar kasar wacce ta shafe shekaru da dama cikin yakin basasa da matsalar karancin abinci.
Ana sa ran shugabannin za su amince da gudummawar kudaden domin gina makarantu da asibitoci da kuma hukumar 'yan sanda.
Burtaniya ta bayyana Somalia a matsayin "kasar da ta fi kowacce rashin tabbas a duniya" amma ta ce a kwai bukatar a sake bata dama.
Al Shabab ba za ta halarta ba
Sakataren harkokin wajen Burtaniya William Hague, ya shaida wa BBC cewa manufar taron ita ce ta tallafawa "kasar da ta ruguje" ba tare da kasashen yamma sun mamayeta ba".
Wannan wani yunkuri ne da Firayim Ministan Burtaniya David Cameron ke jagoranta don nemo sabbin hanyoyin da za a kawo karshen yamutsi da yunwa da yakin basasar da aka shafe sama da shekaru ashirin ana gwabzawa a Kasar.
Wakilai na gwamnatin rikon-kwaryar kasdar da Kungiyoyi daban-daban ne ke halartar taron, amma banda Kungiyar 'yan gwagwarmaya ta Al Shabab wadda ke da ikon mafi rinjayen tsakiya da kuma kudancin Kasar ta Somalia.
A waje daya kuma dakarun Habasha da taimakon sojan gwamnatin rikon kwaryar Somalia sun kwace ikon mulki da birnin Baidoa dake tsakiyar Kasar a hannun mayaka na Kungiyar Kishin Islama ta AlShabab.
Sun kwaci birnin ne salun-alun ba tare da wani fada ba lokacin da mayakan na Al Shabab suka arce daga yankin suna cewar maimakon fadan, za su koma yakin sari-ka-noke
To amma masu aiko da rahotanni sun ce hakan wani babban koma-baya ne ga Kungiyar ta AlShabab.










