bbc.co.uk navigation

Gobara na ci a rijiyar man kamfanin Chevron

An sabunta: 22 ga Fabrairu, 2012 - An wallafa a 21:17 GMT
Rijiyar mai na ci da wuta

Kamfanin mai na Chevron ya ce, rijiyar man sa za ta ci gaba da ci da wuta har zuwa wani lokaci.

Katafaren kamfanin mai na Chevron ya shaidawa BBC cewar gobarar da ta afkawa wata rijiyar mai a tekun Nigeria a watan Janairun da ya gabata, akwai yiwuwar cewa za ta cigaba da ci da wuta a watanni masu zuwa.

Ma'aikatan kamfanin su biyu sun hallaka a lokacin da gobarar ta kama a rijiyar.

Wakilin BBC yace mahukuntan kasar Najeriyar sun cee iskar gas din da ta rika fita ita ce ta haddasa fashewar rijiyar mai wacce ta kama da wuta a tsakiyar watan da ya gabata.

Lamarin dai ana ganin cewa , ya hana al'ummar kauyen Kolouma cigaba da sana'ar su ta kamun kifi.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2012 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.