
Hukumomi sun ce sun kame fursunoni 20 daga cikin 119 da suka tsere
Kungiyar nan ta Jama'atu Ahlussunah Lidda'awati Wal jihad da aka fi sani da Boko Haram ta yi ikirarin kai hari a kan wani gidan Yari a kasar.
Bayanai sun nuna cewa ilahirin 'yan kaso da ke gidan yarin sun tsere banda mutum daya, yayinda kuma aka kashe daya daga cikin masu tsaron gidan kason.
Sai dai a Nasu bangaren hukumomi sun ce sun sake kame wasu daga cikin 'yan kason da suka tsere.
Kakakin hukumar gidan yarin Jihar Kogi ta shaidawa BBC cewa an kame 25 daga cikin wadanda suka tseren.
Ta kuma kara da cewa wadanda aka sake kamawan na hannun 'yan sanda.
Wani jami'in 'yan sanda da ya nemi a boye sunansa ya shaida wa wata jarida a Najeriya cewa kimanin 'yan bindiga 20 ne akan babura suka kai hari kan gidan yarin.
Ya kara da cewa sun shafe kimanin mintina 30 suna kaddamar da harin.
Masu nazarin al'amura na ganin ko ma dai su wanene suka balla gidan yarin akwai yiwuwar sakaci daga jami'an tsaro.









