bbc.co.uk navigation

Bom ya hallaka mutane tara a Somalia

An sabunta: 9 ga Fabrairu, 2012 - An wallafa a 05:39 GMT
Shugaban Somalia, Sheikh Sherif Ahmed

Wani bam ya tashi a kusa da fadar Shugaban Kasar Somalia

'Yan sanda a Mogadishu babban birnin Somalia sun ce wani bam da aka dana a mota kuma aka tayar a kusa da fadar shugaban kasar ya kashe akalla mutane tara.

Jami'ai sun ce, bam din ya tarwatse ne a kusa da Muna Otel, wurin da akasarin lokuta 'yan siyasa da jami'an gwamnati ke ganawa.

Wani mutum mai suna Mohammed Irre ya ga lokacin da bam ya tarwatse kuma ya shaidawa BBC cewa suna zaune lokacin da bam din ya fashe wanda kuma ya girgiza duk fadin yankin.

Kungiyar nan ta masu tsattsauran ra'ayin Islama, Al-Shabab dai ta tabbatar wa da BBC cewa ita ce ta kai harin, amma ta musanta rahotannin farko da ke cewa ta yi amfani ne da dan kunar bakin-wake ne.

Kari a kan wannan labari

BBC © 2012 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.