bbc.co.uk navigation

Wasu na ficewa daga kauyuka a Nijar don kaucewa yunwa.

An sabunta: 8 ga Fabrairu, 2012 - An wallafa a 17:31 GMT

A Jamhuriyar Nijar, yanzu haka mutane da dama ne ke ficewa daga daga kauyuka a jahar Tillaberi wadda aka ambato a sahun gaba wajen matsalar karancin abinci a wannan shekara.

Galibin wadanda ke ficewar dai na shiga birane kamar su Yamai ne don neman abinci.

Rahotanni dai sun nuna cewa akasarin mutanen dake ficewar matane ne da yaransu.

Nijar dai na daga cikin kasashen da hukumar tarayyar Turai ta ce zata taimakawa a yankin Sahel, a Afirka kudu da Sahara, wadanda aka yi hasashen zasu fuskanci matsalar yunwa.

Gwanatin Nijar ta fara saida kayan abinci akan farashi mai rahusa don rage kaifin matsalar

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2012 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.