Gwamnatin Janhuriyar Nigar ta bada sanarwar karin albashi ga ma'aikatanta tare da rage kudin ruwa da na wutar lantarki.
A cewar gwamnatin wannan wani kokari ne na yaki da cin hanci da rashawa kamar yadda shugaba Muhammadou Issaoufo ya yi alkawarin yi a lokacin yakin neman zabensa.
A na dai daukar Niger din a matsayin kasar da bata da wadata, koda yake tana da arzukin yuranium ga kuma man fetur din da ta fara tonowa a karshen shekarar da ta gabata.
To ko mai yasa gwamnatin Niger ta dauki matakin karawa ma'aikatan kasar albashi? Wannan itace tambayar da naiwa kakakin gwamnatin Marou Amadou:









