
Mohammed Abubakar
Kungiyar Kiristoci ta Najeriya wato CAN, ta nuna rashin jin dadinta akan nada Mohammed Abubakar a matsayin sabon Sufeto Janar na 'yan sandan kasar, na wucin gadi.
A cewar kungiyar, bai kamata a ba shi wannan mukamin ba, saboda a cewar ta, yana daga cikin wadanda hukumar bincike akan rikicin Jos na shekara ta 2001, a karkashin jagorancin mai shari'a Niki Tobi, ta gano ya aikata ba daidai ba.
A cikin hirar da yayi da BBC, Pastor Ayo Orisejafor, shugaban CAN din, ya ce bai kamata irin wannan mutum ya rike mukamin Sufeto Janar na 'yan sandan ba.
A tsakiyar wannan makon ne gwamnatin Najeriya ta sanar da nadin Mohammed Abubakar, yayin da ta ce Sufeto Janar Hafiz Ringim ya tafi hutun karshe kamin ya wuce ritaya.







