An kashe mutane goma sha biyar a wani fashi a Zamfara

An sabunta: 26 ga Janairu, 2012 - An wallafa a 20:57 GMT


Rahotanni daga Jahar Zamfara sun ce akalla mutane goma sha biyar ne suka mutu lokacinda wasu da ake jin 'yan fashi ne suka budewa motar da suke tafiya aciki wuta.

Kwamishinan watsa labarai na jihar ya shaidawa BBC cewar haka ma akwai wasu da suka samu raunuka a harin kuma wasu da dama ba'a san inda suke ba.

Lamarin dai ya faru ne a kusa da kauyen Shamusalle na jihar ta Zamfara wanda ke kusa da iyakar jahar da makwabciyar Jihar Katsina.

Maudu'o'i masu alaka

bbc.co.uk navigation

BBC © 2012 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.