
Tashin bama-bamai abu ne da ya zama ruwan-dare a Iraki
Rahotanni daga Iraki sun ce tashin bama-bamai ya kashe akalla mutane ashirin da hudu a birnin Bagadaza.
Ga alamu an kai harin ne yayin wata jana'iza a wata unguwa inda 'yan Shi'a da mabiya Sunnah ke cakude.
Wani jami'in kasar Iraki ya ce wani dan kunar-bakin-wake ne ya tashi wata motar da ke makare da abubuwa masu fashewa.
Har yanzu bayanai na ci gaba da shigowa dangane da harin.







