BBC navigation

Sudan ta Kudu za ta kwace makamai a hannun Kabilu

An sabunta: 20 ga Janairu, 2012 - An wallafa a 07:05 GMT

Mayakan sa kai na Kabila a kasar Sudan ta Kudu

Gwamnatin Sudan ta Kudu ta sha alwashin kwace makaman da ke hannun kabilun da ba sa ga-maciji da juna, bayan tashe-tashen hankulan da suka yi sanadiyyar mutuwar daruruwan mutane a jihar Jonglei.

Ministan yada labarai na kasar, Barnaba Marial Benjamin, ya shaidawa BBC cewa za a kara karfin jami'an tsaro a yankin.

"Tuni jami'an 'yan sanda sun fara isa yankin don ba da kariya ga fararen hula, kuma da zarar an kai isassun jami'an tsaro za a fara karbe makamai a hannun jama'a." In ji Benjamin

A watan Agustan da ya gabata ne dai 'yan kabilar Murle suka kashe 'yan kabilar Lou Nuer, wadanda aka kiyasta yawansu ya kai dari shida

Kasar Sudan ta kudu ta zama sabuwar kasa a duniya a watan Yulin bara, amma a yanzu haka kasar na fuskantar kalubale da dama.

A farko wannan shekarar ne dai mayakan sa kai da ake kira White Army, su ka shiga garin al'ummar Murle inda su ka kashe mutane da kona dukiyoyi da gidaje da dama.

Wannan dai wata ramuwar gayyace ta baya bayaan da aka kaddamar a kasar.

An fara gyaran gine ginen da aka lallata lokacin rikicin, amma sai dauki al'ummar yankin wani dan dogon lokaci kafin su iya manta abu da ya faru.

Da kamar wuya dai a tsayarda ramuwar gaiyya da kabilun biyu ke kaiwa junansu.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.