
Rundunar 'yan sandan kasar na ci gaba da shan suka
Gwamnatin Najeriya ta nemi Sufeto Janar na 'yan sandan kasar Hafizu Ringim ya yi mata bayani cikin sa'o'i 24 kan dalilan da suka sanya wani jigo a kungiyar Boko Haram ya tsere bayan an kama shi.
An nemi Hafizu Ringim ya yi bayani kan abinda ya faru "cikin sa'o'i 24", kamar yadda ministan kula da ayyukan 'yan sanda Caleb Olubolade, ya shaida wa 'yan jarida a Abuja.
"Idan aka same shi da laifi, to shi da kansa zai dandana kudarsa", ya kara da cewa: " Na bayar da umarnin a tsare dukkan jami'an da suke da hannu a cikin lamarin ba tare da bata lokaci ba."
Tunda farko hukumar 'yan sandan Najeriya ta ce wanda ake zargin Kabiru Sokoto, ya kufce ne a lokacin da ake tafiya da shi zuwa gidansa a wajen birnin Abuja domin a gudanar da bincike.
Kungiyar Boko Haram ce ta dauki alhakin harin da aka kai ranar Kirsimeti a majami'ar St. Theresa da ke Madalla a jihar Naija.
An dade ana zargin jami'an 'yan sandan Najeriya da sakaci da rashin kwarewa wurin tunkarar matsalolin tsaron da kasar ke fama da su.
Ko a kwanakin baya sai da shugaba Jonathan ya ce akwai masu goyon bayan kungiyar ta Boko Haram a jami'an gwamnatinsa da jami'an tsaron kasar da kuma fannin shari'a.
Ana dai ci gaba da zaman dar dar a garin na Abaji.
A yanzu haka jami'an tsaro na sintiri da motoci masu sulke a garin na Abaji, inda a wasu wuraren jama'a basu fita daga gidajensu.
Bin diddigi
’Yan sandan dai suna zargin mutumin ne mai suna Kabiru Sakkwato da hannu a harin bom din da aka kai ranar Kirsimeti a majami’ar ta St Theresa da ke garin Madallah, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar fiye da mutane arba’in.
"Na bada umarnin a ci gaba da tsare dukkan jami'an tsaron da ke da alaka da tserewar mutumin. "
Ministan 'yan sanda Caleb Olubolade
Rahotanni sun nuna cewa an kama mutumin ne a gidan gwamnatin jihar Borno dake Abuja.
Jami'an tsaron Najeriya, sun ce da ma sun dade suna bin diddigin mutumin, kafin a kai samamen hadin gwiwar da ya kai ga kama shi.
Rundunar ta kuma ce tuni ta dakatar da kwamishinan 'yan sandan da aka dorawa alhakin tsare shi, kuma idan bincike ya nuna cewa shi da yaransa sun aikata laifi to za a gurafanar da su a gaban kotu.
Kamu da kuma tserewar tasa na zuwa ne a daidai lokacin da jami'an tsaron Najeriya ke ci gaba da shan suka saboda gazawarsu wajen shawo kan matsalar tsaro da ta addabi kasar, musamman hare-haren da ake zargin 'yan kungiyar ta Boko Haram da kaiwa.
A wata sanarwa mai dauke da sa-hannun kakakin hedkwatar ’yan sandan ta kasa, Olusola Amore, rundunar ta ce an danka mutumin ne ga wani kwamishinan ’yan sandan don ya ci gaba da gudanar da bincike.

Cocin da aka kaiwa hari ranar Kirsimeti a garin Madalla
A yayin gudanar da binciken ne, in ji Mista Amore, kwamishinan ya mika mutumin ga wasu yaransa wadanda ya baiwa umurnin kai wanda ake zargin garin Abaji na Yankin Babban Birnin Tarraya, inda wasu ’ya’yan kungiyar ta Boko Haram suka yi dirar mikiya akanayarin ’yan sandan suka kuma kubutar da mutumin.
A wani bangare kuma, wata kotu babbar kotun tarayya dake Abuja ta bada belin wasu mutane 6 da ake zargin cewa 'ya'yan kungiyar Boko Haram ne.
Ana tuhumarsu da tada wani bom a ofishin hukumar zabe dake garin Suleja na jihar Niger, a ranar 8 ga watan Afrilun shekarar data gabata.
Ana kuma zarginsu da jefa bomb a wani wurin gangamin siyasa a garin Sulejan, a ranar 3 ga watan Maris da ya gabata.
Za a ci gaba da sauraron karar a ranar 7 ga watan Fabrairu mai zuwa.
A Maiduguri kuma rundunar tsaro ta hadin gwiwa ta ce ta ta kama wasu manyan jami'an Boko Haram, bayan wani harin da suka kai, inda sojoji biyu suka hallaka.









