
Shugaba Hamid Karzai
Shugaban Afghanistan Hamid Karzai ya ce zai kyale 'yan kungiyar Taliban su bude ofis a kasar Qatar,a wani yunkuri na taimakawa shirin wanzar da zaman lafiya.
Wannan dai shi ne karon farko da shugaba Karzai ya nuna goyon bayansa a bainar jamaa ga wannan batu.
Sai dai fadar shugaban ta ce ya kamata a hana duk wata kasar waje yin katsalanda a tattaunawar zaman lafiya.
A kwanan nan dai wasu rahotannin sun nuna cewa Amirka da wasu kasashe dake sojoji a kasar ta Afghanistan, suna kokarin yin tasu tattaunawar ta dabam da 'yan Taliban .
Kawo yanzu dai kungiyar ta Taliban ba ta ce uffan game da wannan batu ba.









