BBC navigation

Yarima Philip na samun sauki

An sabunta: 24 ga Disamba, 2011 - An wallafa a 14:51 GMT
Yarima Philip, maigidan sarauniyar Ingila

Yarima Philip, maigidan sarauniyar Ingila

Iyalan masarautar Birtaniya, na zuwa duba maigidan sarauniyar Ingila, Yarima Philip, wanda ke kwance a asibiti bayan anyi masa tiyata a zuciyarsa.

Sarauniya Elizabeth da 'yayanta maza da mace daya dukkansu sun je asibitin dake kusa da garin Cambirdge, inda yarima Philip ke jinyar aikin da akai masa na toshewar wani bangare na zuciyarsa:

Wakiliyar BBC ta ce wannan itace ziyara ta farko da akai kaiwa yarima Philip tun bayan da aka akai shi asibitin a jiya.

Yanzu haka dai ance yana samun sauki. Sai dai kuma ba'a tabbatar ko zai iya zuwa Sand-ringham domin yin bikin kirsimeti tare da sauran iyalan masarautarba kamar yadda aka saba.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.