
Dakarun Amurka na karshe na ficewa daga Iraqi
Dakarun Amurka na karshe dake ficewa daga kasar Iraqi sun ketara zuwa Kasar Kuwait, abinda ke kawon karshen mamayar da Amurka tayi a Iraqin na tsawon shekaru kusan tara da hambarar da Marigayi Saddam Hussein.
Tun a bara ne dai sojojin Amurka suka daina kai hare-hare, inda suka mika ragamar aikin ga sojojin Iraqi.
Akalla sojojin Amurka 4,500 ne suka mutu sannan wasu dubun-dubatar 'yan Iraqi suma suka rasa rayukansu tun lokacin da Amurka ta jagoranci yakin a shekara ta 2003, sannan Amurkar ta kashe kusan dala tiriliyan daya a yakin.
Yayinda akasarin 'yan Iraqin su kai imanin cewar lokaci ya yi na Amurkawan su tattara ina-su ina-su su bar Kasar, sai dai wasu da dama kuma na cikin damuwa game da kalubalen da suke tunanin za'a fuskanta a nan gaba









