bbc.co.uk navigation

An rantsar da Joseph Kabila

An sabunta: 20 ga Disamba, 2011 - An wallafa a 15:39 GMT

An rantsar da Shugaba Joseph Kabila na Jamhuriyar Demokuradiyar Congo bayan da ya yi ikirarin samun nasara a zaben Shugaban kasar dake cike da cece -kuce da aka yi a watan da ya wuce.

Da ya ke rantsuwar kama aikin Shugaban kasar, Mr Kabila ya yi alkawarin kare hakkin 'yan kan kasar:

Sai dai jagoran 'yan adawa, Etienne Tshisekedi, ya hakkake cewar shi ya lashe zaben, kuma ya ce zai rantsar da kansa nan gaba a cikin satin nan.

Shugabannin kasashen Afrika kalilan ne suka halarci bukin.

Dukannin jakadun kasashen waje dake kasar dai an kira su da su halarci bukin rantsarwar ko kuma ba'a san da kasancewarsu a kasar ba.

Masu sa ido kan zaben na cikin gida da kuma waje sun yi tir da magudin da aka tabka a zaben.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2012 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.