BBC navigation

Shugaba Ouattara ya yi bayani kan mika Gbagbo

An sabunta: 1 ga Disamba, 2011 - An wallafa a 20:54 GMT
Shugaba Ouattara

Shugaba Ouattara na Ivory Coast

Shugaban Ivory Coast, Alassane Ouattara, ya mayar da martaninsa na farko game da kai magabacinsa, Laurent Gbagbo, Kotun manyan laifuka ta duniya, yana cewar, an yi duk abinda ya kamata domin gujewa ci masa fuska.

Ya ce barin kotunan duniya su yi wa tsohon shugaban kasar shari'a, zai kasance hanyar da ta fi da cewa don tabbatar da cewar an yi masa shari'ar adalci, da kuma kaucewa zargin shari'ar bi-ta- da -kulli.

Ya yi kalamin ne a lokacin wata ziyara zuwa Guinea -Conakry mai makwabtaka.

Ranar Talata ne aka mika Mr Gbagbo, kuma ana sa ran zai yi bayyanarsa ta farko a gaban kotun ranar Litinin mai zuwa.

Zaben da Mr Gbagbo ya shirya, aka kuma bayyana cewar ya fadi, kuma ya ki sauka, shi ya tsunduma kasar ta Ivory Coast cikin rikicin siyasa, wanda ya haddasa asarar rayuka.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.