bbc.co.uk navigation

Girka ta zabi sabon pira minista

An sabunta: 10 ga Nuwamba, 2011 - An wallafa a 15:41 GMT
Lucas Papandemos

Lucas Papandemos

A kasar Girka an bayyana sunan Lukas Papademos, a matsayin praministan rikon kwarya.

A da Mr Papademos, mataimakin shugaban babban bankin tarayyar turai ne.

Yanzu haka shugaban kasar ya neme shi da ya kafa sabuwar gwamnation hadin kan kasa, gwamnatin da zata aiwatar da yarjejeniyar da aka cinma da tarayyar turai kan agajin da za a baiwa Girkar.

Hakan na faruwa ne yayinda Tarayyar Turai ta rage girman habakar tattalin arzikin da aka yi hasashe a kasashe masu amfani da kudin euro a badi, daga kashi daya da digo takwas cikin dari zuwa rabin kashi guda kacal cikin dari.

Wani babban jami'i na tarayyar turai ya yi gargadin cewa an samu tsaiko a bunkasar tattalin arzikin, kuma ana fuskantar hadarin sake fuskantar koma-bayan tattalin arziki.

Kari a kan wannan labari

BBC © 2012 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.