
Nicolas Sarkozy
Shugaban Faransa, Nicolas Sarkozy, ya ce kuskure akayi da aka amince da Girka ta shiga kungiyar Tarayyar Turai a shekara ta 2001.
A wata hira da yayi da gidan talabijin na Faransa, Sarkozy ya ce bai kamata a shigar da Girka cikin kungiyar ba saboda abunda ya kira: karairayin da ke cike da alkalumman tattalin arzikin ta.
Kalaman nasa sun zo ne kwana guda bayan shugabannin kasashen turai sun cimma yarjajeniyar magance matsalar bashi a nahiyar ta turai.
A murtanin da ya mayar, ministan harkokin wajen Girka, Stavros Lambrinidis, ya ce ba kasarsa ce tushen matsalar kudaden da kasashen yankin Euro ke fuskanta ba.