An sabunta: 8 ga Mayu, 2011 - An wallafa a 20:19 GMT

CPC ta nemi a soke zaben shugaban kasa

A Najeriya, Jam'iyar adawa ta CPC ta shigar da kara yau a gaban kotun sauraren kararrakin zaben shugaban kasa, inda take kalubalantar zaben shugaba Goodluck Jonathan, a matsayin wanda hukumar zaben INEC ta ce shi ne ya lashe zaben da aka gudanar a watan jiya.


Jam'iyyar ta CPC ta ce hujjojinta na shigar da karar sun hada da zargin tafka magudi, da kuma rashin bin dokokin zabe, inda ta ce zata gabatar da shaidu 151 a karar da ta shigar.


Da ma dai dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar ta CPC , Janar Muhammadu Buhari, ya ce shi a matsayinsa, ba zai shigar da kara kan sakamakon zaben ba, sai dai jam'iyyarsa, in ta ga dama.

bbc.co.uk navigation

BBC © 2012

BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.