An sabunta: 26 ga Satumba, 2010 - An wallafa a 17:23 GMT

Harkar Noma a Najeriya

Gonar shinkafa

Najeriya ita ce kasa ta 20 a duniya kuma ta 1 a nahiyar Afirka wajen noma da samar da abinci.

Sai dai kuma a yanzu haka kasar bata iya ciyar da al'ummarta sama da miliyan 140, sai ta hada da shigo da abinci daga kasashen ketare.

Yin watsi da noma da gwamnatocin baya suka yi na shekara da shekaru shi ne ummul'aba'isin koma bayan da aka samu ta fuskar noma a kasar.

Ko da yake duk da haka har yanzu Najeriya na samun kashi 26.8% na arzikinta daga wannan fani.

Yanzu haka Najeriya bata fitar da Koko, Gyada, Roba da Manja kamar yadda take kafin shekarun 1970.

Wannan kuwa a cewar masana tattalin arzuki ya farune saboda da rashin kulawar da gwamnatoci musamman na soji suka yiwa harkar noma.

BBC navigation

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.