An sabunta: 8 ga Yuli, 2010 - An wallafa a 16:16 GMT

Kotu ta hana a mika Abu Hamza ga Amirka

Abu Hamza al Masri

Ana zargin Abu Hamza ne da ta'addanci

Wata kotun kare hakkin dan Adam ta Tarayyar Turai ta bada umarnin dakatar da mika wani mai wa'azin musulunci mai kaifin ra'ayi ga Amurka daga Birtaniya bisa zargin ta'addanci.

Mai wa'azin, Abu Hamza al- Masri na zaman wakafi na shekaru bakwai yanzu a Birtaniya, bisa laifukan da suka hada da tunzura yin kisan kai.

Masu gabatar da kara a Amurka na zarginsa da yunkurin kafa sansanin horar da 'yan ta'adda da kuma kasancewa da hannu a sace wani dan Yemen wanda hakan ya kai ga mutuwar mutane hudu da aka yi garkuwa da su.

BBC navigation

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.