An sabunta: 21 ga Yuni, 2010 - An wallafa a 07:45 GMT

An kaddamar da asusun tallafawa Nijar

Asusun tallafawa masu fama da yunwa a Nijar

Kungiyoyin bada agaji biyu sun kaddamar da asusun gaggawa domin tallafawa masu fama da yunwa a jamhuriyar Nijar

Wasu manyan kungiyoyin bada agaji guda biyu sun kaddamar da gidauniyar agajin gaggawa domin tallafawa miliyoyin mutanen da ke fama da yunwa a jamhuriyar Nijar.

Kungiyoyin na Save the Children da Oxfam sun ce lokaci bai kure ba, a kokarin kaucewa sake faruwar yunwar da ta jefa kimanin mutane miliyan uku da rabi cikin halin kaka-ni-kayi shekaru biyar da su ka gabata a jamhuriyar ta Nijar.

Wakiliyar Majalisar dinkin duniya a jamhuriyar Nijar Khardiata Lo Ndiaye ta ce halin da ake ciki ya dara na farin shekara ta 2005.

Matsalolin da suka hada rashin kyawun amfanin gonar da aka samu a shekarar bara da kuma harhawar farashin kayayyaki ne suka jefa Nijar cikin halinda take ciki

Majalisar dinkin duniya ta nanata cewar ana bukatar kudaden da za'a tallafawa kasar ba tare da wani bata lokaci ba

BBC navigation

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.