Shekaru 25 na mulkin Al-Bashir a Sudan

10 Yuli 2014 An sabunta 17:00 GMT

Shekaru ashirin da biyar kenan da Omar Al Bashir ya kwace ragamar mulkin kasar Sudan. Babban jami'in na Soja ya sha tsallake yunkurin juyin mulki da bore da kuma ballewar Kudancin Sudan a shekara ta 2011.

To, amma a zamanin mulkinsa a matsayin Shugaban kasa mutane da dama sun koka da wahalhalu iri-iri da su kan fuskanta.