Yaki da cutar Ebola a Yammacin Afrika

2 Yuli 2014 An sabunta 09:50 GMT

Hukumar lafiya ta duniya- WHO ta yi kira a dauki matakan da suka dace ton yakar cutar Ebola wacce ta barke a Yammacin Afrika, cutar da ta kashe mutane kusan 400.
Sylvain Cherkaoui/Cosmos/MSF
Hukumar lafiya ta duniya- WHO ta yi kira a dauki matakan da suka dace ton yakar cutar Ebola wacce ta barke a Yammacin Afrika, cutar da ta kashe mutane kusan 400. Wannan ne lokacin da cutar ta fi yaduwa da kuma kashe mutane.
Garin Gueckedou a Guinea.Sylvain Cherkaoui/Cosmos/MSF
Mutane kusan 600 sun kamu da cutar a Guinea tun bayan da cutar ta barke watanni hudu da suka wuce a Guekedou, watau cibiyar da ake hada-hadar kasuwanci a kasar.
An kula da marasa lafiya. Sylvain Cherkaoui/Cosmos/MSF
Kungiyar agaji ta Medecins Sans Frontieres ta yi gargadin cewar cutar Ebola ta yi matukar yaduwa. A cewar kungiyar, ma'aikatanta kusan 300 na taimaka wa a kasar ta Guinea.
kula da marasa lafiya. Sylvain Cherkaoui/Cosmos/MSF
Kwayar cutar Ebola tana janyo zazzabi, da kasalar jiki da matsalar gabobi da kuma ciwon makogwaro, kamar yadda hukumar lafiya ta duniya ta bayyana.
kula da marasa lafiya. Sylvain Cherkaoui/Cosmos/MSF
Kwayar cutar na yaduwa kuma ba tada magani, a don haka ma'aikatan lafiya na saka kayayyakin kariya domin kada su kamu da cutar.
Cikin sa'a daya ake gano kwayar cutar Ebola sakamakon gwaje-gwaje a asibiti.
Ana sakawa tufafi da takalma sinadarin Chlorine domin rage kaifin kwayar cutar ta Ebola.
Baya ga kulawar gaggawa a asibitoci, tawagar likitocin na wayar da kan jama'a a kauyuka irinsu Touloubengo saboda da zarar mutum ya soma jin alamun cutar, ya garzaya asibiti.
Sia Bintou ta shafe kwanaki 10 tana samun kulawa a asibiti, likitoci sun caji cewar ba za ta sha ba, amma kuma daga karshe ta ci galabar cutar.
Mutane da dama sun rasu. A nan iyalan gidan Finda Marie Kamano ne ke makokin rasuwar daya daga cikin 'yan gidan.
Ana saka alamu a kaburbura domin tantance wadanda cutar ta hallaka.