Harin bama-bamai a kasuwar Jos

21 Mayu 2014 An sabunta 10:13 GMT

Hukumomi a Nigeria sun tabbatar da mutuwar mutane akalla 118 a wani hari da aka kai a Jos babban birnin jihar Filato a ranar Talata.
Hukumar bayar da agajin gaggawa ta Nigeria ta ce, adadin wadanda suka mutu a Jos da ke jihar Filato ya kai 118 a harin da aka kai.
Jami'an ayyukan gaggawa da kuma jama'a sun taimaka wajen kashe wutar da ta kona wani bangare na kasuwar sakamakon tashin bama-bamai biyu a ranar Talata.
Kawo yanzu babu cikakkun alkaluma game da adadin mutane da suka rasu a wannan harin bam din.
Bama-bamai biyu ne suka fashe a kusa da kasuwar Terminus da kuma babban asibitin birnin Jos na jihar Filato.
Mutane da dama sun samun raunuka bisa fargabar abinda ya faru, wasu kuma sun gudu sun bar abubuwansu don su tsira da ransu.
Shugaban Nigeria, Goodluck Jonathan ya yi Allah wadai da harin da aka kai a Jos, inda ya ce gwamnatinsa za ta ci gaba da yaki da ta'addanci.
Tashin bam ya Jos ya cefa tsoro ga al'ummar birnin saboda ana dade ana fama da rikici mai nasaba da addinni da kabilanci a jihar Filato