Wasu 'yan matan Chibok da suka tsira

8 Mayu 2014 An sabunta 13:54 GMT

'Yan Boko Haram sun sace 'yan mata fiye da 200 a makarantar sakandare ta Chibok, inda kusan 50 suka kubuce daga hannun 'yan bindigar.
Uwargidan gwamnan jihar Borno, Hajiya Nana Kashim ta ziyarci garin Chibok inda ta tattauna da iyayen wasu daga cikin 'yan matan da aka sace.
Wasu daga cikin 'yan matan da suka kubuce daga hannun 'yan Boko Haram lokacin da aka sace su a makarantarsu a ranar 14 ga watan Afrilu.
'Yan mata fiye da 50 ne suka kubuta daga cikin 276 da 'yan Boko Haram suka sace a makarantar sakandare ta Chibok da ke jihar Borno.
Daya daga cikin 'yan matan da suka kubuce, ta bayyana yadda lamarin ya faru a cikin daren da 'yan Boko Haram suka kutsa cikin makarantarsu.
Shugabannin al'ummar Chibok sun yi jawabai don kwantar da hankalin iyayen daliban da aka sace.
Gwamnan jihar Borno, Kashim Shettima ya ziyarci garin Chibok 'yan kwanaki bayan afkuwar lamarin.
'Yan Boko Haram sun bankawa ajujuwa wuta bayan da suka sace daliban.
An kona wajen kwanan daliban kurmus, a yayinda 'yan Boko Haram ke kara jan kunnen yara su daina karatun Boko.
Daruruwan mata ne ke zanga-zanga a fadin Nigeria don matsawa gwamnati lamba ta maida hankali wajen ceto 'yan matan.