BBC navigation

Zakanya ta tsallaka babban kogi

An sabunta: 11 ga Maris, 2014 - An wallafa a 14:18 GMT

Rayuwar zakanya a Kogi

  • Mai daukar hotunan namun daji na Girka, Kyriakos Kaziras ya dauko hoton wata zakanya wacce ta tsallaka wani kogi tare da 'yarta, a gandun dajin Masai Mara dake Kenya
  • Ta rike 'yarta a bakinta domin kai wa gabar kogin ba tare da matsala ba.
  • Zakuna a koda yaushe suna kokarin kubutar da 'ya'yansu daga fuskantar hadura.
  • Zakanya na farauta a cikin dare inda take kashe wasu namun daji domin yin kummallo.
  • Ana rainon 'ya'yan zakuna na tsawon shekara guda kafin a yaye su.
  • Akwai zakuna da dama a gandun dajin Kenya da Tanzania da kuma wasu makwabtan kasashe a yankin gabashin Afrika.
  • A cikin gandun dajin Masai Mara, ana barin zakuna su yi walwala ba tare da tsangwama ba.

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.