Hotunan hakar kaburbura a Somaliland

3 Maris 2014 An sabunta 16:04 GMT

Hotunan tonon kaburbura, domin gano shaidun aikata kisan mutane da dama, da aka taba yi a babban birnin lardin Somaliland.
An gano ƙasusuwan mutane ne da dama a wani babban kabari a Hargeisa, babban birnin Somaliland
Yankin Somaliland ya ayyana 'yancin kai ne a shekarar 1991, bayan tumbuke gwamnatin Siad Barre. A karshen mulkinsa an hallaka dubban jama'a, kuma an ruguje garuruwa, bayan wani tawayen da aka yi.
Ana ci gaba da aiki akan kasusuwan wadanda aka kashe
A wani babban kabari a Hargeisa, babban birnin Somaliland, ana ci gaba da tono kasusuwan mutane, wannan wani yunkuri ne na daliban Peru masu binciken abubuwan da suka faru a baya ta hanyar tono abubuwa daga kasa.
A daya daga cikin kaburburan an tono kasusuwan mutane shida
A daya daga cikin kaburburan an tono kasusuwan mutane shida. Daliban da suke binciken sun gano kasusuwan mutane 44, amma zasu ci gaba da tona wasu kaburburan.
Wadannan tutoci ne a aka kafawa kowacce shaida da aka samu
"Hargeisa wani babban makabarta ne", inji Jose Pablo Baraybar, wanda ke jagorantar binciken. " Wasu sun ce akwai gawawwaki kimanin dubu 200 binne, amma babu wanda ya san ainihin yawansu."
Masu binciken suna amfani da burushi wajen goge kasusuwan da aka gano
Masu binciken suna amfani da burushi wajen goge kasusuwa da hakora da aka tono cikin tsanaki.
Ana tankade kasar cikin kaburran
Ana tankade kasar wurin da ake binciken , domin baiwa masu binciken damar gano kananan kasusuwa, da gashi da zasu taimaka wajen gane mamatan.
Ana auna ƙoƙon kai
Ana auna kasusuwan da aka gano, domin gane asalin mutanen da kuma ko maza ne ko mata.
Wani kashin ƙugu ya nuna alamun harbin bindiga
Wasu kasusuwan na bada haske kan yadda aka kashe wasu mutanen. Wani kashin ƙugu ya nuna alamun harbin bindiga.
Birnin Hargeisa
Somaliland yanki ne mai kwarya-kwaryan 'yan ci. Wannan ya baiwa yankin damar samun kudaden gudanar da wannan bincike domin hukunta wadanda suka aikata.
Yusuf Muhammed Duwali
Yusuf Mohamed Duwali, dan shekaru 80 ya shaida tono wasu kaburbura biyu a kusa da gidansa a Hargeisa. Ya ce, a kullum ina wuce kaburburan da aka tono a hanyar gidana.
Wani dan sanda na runduna ta musamman da ya ke gadin wurin
Wani dan sanda na runduna ta musamman da ke gadin wurin.
Wani dalibi ya na nazari akan kasusuwan wani mutum.
Ana amfani da lambobi wajen fayyace kasusuwan mutanen. Za a tabbatar da gano musabbabin mutuwar mutanen, shekarun mamatan, da kuma ko maza ne ko mata.