Bukin Sallar Shanu a Kamaru

6 Janairu 2014 An sabunta 13:03 GMT

Bukin Sallar Shanu a Jamhuriyar Kamaru wanda aka yi a Ngaoundere a karshen watan Disambar 2013.
Shanu
Daga ranar 19 zuwa 21 ga watan Disambar 2013 aka gudanar da bukin sallar shanu a Ngaoundere na kasar Kamaru
Sarakuna
Bukin ya samu halartar sarakunan gargajiya: Lamidon Adamawan Najeriya Dr Barkindo Aliyu Musdafa da kuma Alhadji Mouhamadou Hayatou Issa Lamidon Ngaoundere (Adamaouan Kamaru)
Masu rike da sauratun gargajiya daga jihohin Taraba da Borno a Najeriya suma sun shiga kasar Kamaru don halartar bukin.
Wanda ya shirya bukin Alhadji Mouhamadou Abbo Ousmanou tare da wasu manyan jami'an gwamnatin Kamaru.
Fulani daga sassa daban daban na kasashen Afrika sun halarci bukin sallar shanu a Kamaru. Galibinsu sun yi ado irinna Fulako.
'Yan matan fulani suma sun je wajen bukin, sanye da kaya irin na gargajiya.
Kofar fadar Lamidon Ngaoundere na Kamaru, Alhadji Mouhamadou Hayatou Issa inda aka lillika hotunan Lamidon Adamawan Najeriya, Dr Barkindo Aliyu Mustapha.
Matasan Fulani sun nishadantar da jama'a da su ka je kallon bukin sallar shanu a Kamaru.
An yi abincin gayya inda mata suka tuka tuwo malmala-malmala don baiwa bakin da suka halarci bukin.
Hadja Mata daya daga cikin shugabannin girke-girke na abincin gargajiya a bikin shanun da Alhadji Abbo ya hada.
An gasa raguna da shanu, don mutane su ci nama iya yadda za su iya.
Cin abinci dare a Gidan Alhadji Abbo, bayan an yini ana bukukuwa irinta Fulani a Ngaoundere.