Wanda ya kirkiri bindigar AK 47 ya rasu

23 Disamba 2013 An sabunta 17:50 GMT

Fitaccen dan kasar Rashar nan da ya kirkiro bindigar AK 47, wato Mikhail Kalashnikov ya mutu yana da shekaru 94 a duniya.
Wani mayaki na harba bindigar AK 47 a garin Bhamdoun bayan da yaki ya barke sakamakon ficewar Isra'ila daga yankunan kiristoci.
Dan yaro na shan sigari rige da bindigar AK 47 a ranar 5 ga watan Afrilun 1987, bayan Chadi ta ci Libya da yaki.
Sojin sa kai a Bucharest rike da bindigar Kalashnikov lokacin zanga-zangar kin jinin tsarin kwaminisanci.
Tsohon shugaban Iraki Saddam Hussein rike da AK 47 lokacin wata ziyara da ya kai kauyensu.
Sojin Albania a kusa da kauyen Shoshaj na Yugoslavia lokacin yakin Kosove da Serbia.
Mikhail Kalashnikov wanda ya kirkiri AK 47 lokacin bukin zagayowar shekaru 55 da kirkirar bindigar wato a ranar 23 ga watan Nuwambar 2003.
Dakarun Serbia lokacin rangadi a yakin basasan Yugoslavia.
Wasu matasa rike da AK 47 cikin dakarun Janar Dostum a arewacin Afghanistan a shekarar 1996.
'Yan tawayen Kashmir rike da AK 47 a shekarar 1990.
Sojin kasar Nicaragua na harba bindiga a kan 'yan tawayen Sandinista a shekarar 1993.
Sojojin sa kai na Jordan rike da bindigogin AK 47 lokacin yakin tekun fasha a shekarar 1991.
'Yan tawaye su na harba AK 47 lokacin da suke tafiya a jerin gwano kusa da Bani Walid a Libya a shekarar 2011.
Wani tsoho na goge bindigarsa AK 47 lokacin yakin hambarar da Gaddafi a gabashin Sirte.
Bindigogi kirar Kalashnikov wadanda aka kwace daga gungun masu aikata laifuka na Mexico wadanda aka shafawa ruwan zinare.