BBC navigation

Juyin mulkin soji a kasar Chile

An sabunta: 11 ga Satumba, 2013 - An wallafa a 10:41 GMT

Hotunan: Juyin Mulkin soji a Chile

 • Salvador Allende daga 1908 zuwa 1973
  A ranar 11 ga watan Satumba, Shugaba Salvador Allende na Chile, zababben shugaban kasa na farko a duniya mai bin tafarkin gurguzu ya mutu sakamakon boren da sojoji suka yi.Bayan zabensa a shekarar 1970, ya bullo da sauye-sauyen tattalin arziki abinda ya bakanta ran 'yan adawa
 • Ma'aikatan hako ma'adinai na zanga-zanga a ranar 20 ga watan Yuni 1973.
  Kokarinsa na sake fasalin tattalin arzikin kasar ya janyo hauhawar farashin kayayyaki da kuma karancin abinci. Inda aka yi yajin aikin daya gurgunta kasar. Daga nan kuma sai aka kifar da gwamnati.
 • Janar Augusto Pinoche a hagu tare da Shugaban Chile, Allende
  A watan Agustan 1973, Allende ya nada manya sojoji a gwamnatinsa a kokarin murkushe boren. A lokacin Janar Augusto Pinochet ne babban hafsan sojin kasa.
 • Dakarun na gani fadar shugaban kasa
  Manyan jam'iyyun adawa biyu sun yi kira ga shugaban kasar ya yi sauka a yayinda Allende ya bukaci magoya bayansa su fito don nuna mubaya'a
 • Dakarun kasar Chile sun ja daga.
  An kaiwa fadar shugaban kasa hari da rokoki da bambamai da tankunan yaki, bayan da shugaban kasar yaki amincewa ya yi murabus
 • Dogaran shugaba Allende masu neman kareshi daga mahara
  Majiyoyin soji sun ce, Alllende ya bukaci a bashi minti biyar don ya yi murabus, amma sai dakarun soji suka ki yarda.
 • Fadar shugaban kasa a La Moneda
  An dasa akalla bambamai 17 a fadar shugaban kasa.Hukumomi sun ce Shugaban ya harbi kansa bayan da sojoji suka diranma fadarsa
 • Sojin Chile na suntiri a babban birnin kasar Santiago a ranar 4 ga watan Oktoba, 1973. AFP
  An kafa dokar hana fita a fadin kasar sannan aka haramta daukar bindiga.
 • Janar Augustom Pinochet a jerin gwanon motoci a Santiago a ranar 11 ga watan Satumbar 1973 jim kadan bayan juyin mulkin da aka kashe Shugaban Allende. AFP
  Janar Augusto Pinochet wanda ke cikin dakarun da suka yi juyin mulki ya ayyana kansa a matsayin sabon Shugaban kasa. Duka 'yan majalisar zartwarsa sojoji ne.
 • Dakarun Chile na rangadi a kan titunan birnin
  Rahotanni sun nuna cewar dubban mutane sun mutu amma sojoji sun ce adadin bai kai 100 ba, a juyin mulkin da hukumar leken asiri ta Amurka CIA ta goyi baya.
 • Fadar shugaban kasa a La Moneda na karkashin matakan tsaro
  Pinochet ya yi mulki na tsaro shekaru 17, inda sojoji suka kashe 'yan adawa fiye da 3,000 wasu kuma suka bace.

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.