Rayuwar al'ummar Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya

21 Agusta 2013 An sabunta 16:02 GMT

Wata mata tare da unguwar-zoma suna kokarin gudanar da rayuwa a yanayi mai cike da rudu a Afirka ta Tsakiya, lamarin da ya bar akasarin 'yan kasar ba tare da samun kiyon lafiya ba.
Chimene Kpakanale da jaririnta a asibitin Obi da Merlin ke daukar nauyinsa a Afirka ta Tsakiya
Ana ganin Chimene Kpakanale, mai shekaru 22 a duniya, a matsayin daya daga cikin matan da suka yi sa'a a Afirka ta Tsakiya, saboda ta haifi danta na uku cikin sauki a asibiti. An tilastawa wasu matan barin gidajensu saboda hatsaniyar da aka yi sakamakon juyin mulkin da 'yan tawaye suka yi a watan Maris. Hakan ya sanya mata da dama sun haihu a cikin daji ba tare da samun taimakon kwararru ba.
Chimene Kpakanale  da jaririnta suna  fakewa a karkashin malafa a garin Obo na Afirka ta Tsakiya.
Ko da a lokacin da ake zaman lafiya a Afirka ta Tsakiya, kasar tana daga cikin kasashen da aka fi fama da mutuwar kananan yara; hasalima duk yaro daya cikin yara goma ba ya yin shekara daya a duniya. Yanzu dai Majalisar Dinkin Duniya ta ce kasar ta nuna duk alamun da za su sanya ta cikin kasashen da suka wargaje sakamakon rashin doka da oda tun lokacin da 'yan tawayen Seleka suka hambarar da Shugaba Francoise Bozize.
Chimene Kpakanale tana gabatar da jaririnta ga makwabtanta a Obo da ke Afirka ta Tsakiya
Ms Kpakanale da mijinta da kuma 'ya'yanta guda uku suna zaune ne a garin Obo, wurin da 'yan tawayen Lord's Resistance Army(LRA), wacce Joseph Kony ke jagoranta suka fi karfi. Rashin kwanciyar hankalin da aka kwashe shekaru da dama ana fama da shi a kasar ya bai wa masu tayar da kayar-bayan Uganda damar kafa sansanoni a yankin. Ms Kpakanale ta ce gudanar da rayuwa a karamin garin tana da wuya, musamman daga watan Maris lokacin da 'yan tawayen LRA suka tsananta kai hare-hare. Zaman da 'yan tawayen suka yi a Obo ya sanya garin ya zama saniyar-ware daga sauran yankunan kasar saboda babu wanda ke iya yin balaguro ta hanyoyin yankin.
Wadansu yara a kusa da wani gida a garin Obo na Afirka ta Tsakiya.
Abubuwan more rayuwa sun yi karanci a Obo saboda 'yan gudun hijra na tserewa daga babban birnin kasar, Bangui suna zuwa garin wanda ke kimanin kilomita 900 daga Bangui. Da zarar mutane sun suna jin matukar tsoron barinsa domin haka ne mutane suka durfafi noma a gonakin da ba su da yawa. Hakan dai ya sanya Ms Kpakanale da sauran mutanen garin Obo na fukantar karancin kudi da abinci.
Wani yaro da ake yi wa gwajin karancin abinci mai gina jiki a asibitin da ke sansanin Batalimo na Afirka ta Tsakiya wanda Merlin ke tallafawa
A kudu maso yammacin kasar, ana fama da tashin farashin kayan abinci, musamman a garin Batalimo, wanda ke da nisan kilomita 70 daga babban birnin kasar. Anatole Nzu, mai shekaru 32 a duniya, likita ce sansanin 'yan gudun hijira wanda aka kafa a garin Batalimo domin tsugunar da mutanen da gujewa rikicin da ake yi a Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo. Asibitin sansanin, wanda a can ne al'umar garin ke karbar magunguna, yana ba da magunguna ga mutanen da suka samu raunuka sakamakon boren da 'yan tawayen Seleka suka yi.
ma'aikacin asibiti
Sata da kwacen kayayyaki sun tilastawa mutane da dama ciki har da akasarin ma'aikatan agaji 'yan kasashen waje da ma'aikatan kiwon lafiya gujewa daga kasar.
Dakin shan magani
A wani lokaci magunguna ba za su wuce na kwanaki 75 ba, sannan kuma yanayin tsaro ya lallace ta yadda duka motocin da ma'aikatan agaji ke amfani dasu a dauke zuwa Jamhuriyar Demokradiyar Congo
Marasa lafiya na jiran a bude asibiti
Kusan watanni shida bayan 'yan tawaye sun kwace iko, mutane da dama suke yin dogon layi suna jira a bude asibiti tunda sanyin safiya
Anatole Nzu
Mista Nzu wanda yazo daga Batalimo na Jamhuriyar Demokradiyar Congo a shekara ta 2009, na ganin cewar ya yi sa'a tun da matarsa da 'ya'yansa shida sun tsira
Sansanin 'yan gudun hijira na Batalimo
Akalla kashi daya cikin uku na al'ummar Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya na bukatar tallafin abinci da wajen kwana da kuma lafiya.
Jaririn Chimene Kpakanale
Mutuwar jarirai ya rubanya sau uku a kasar sakamakon tashin hankali da kuma matsalolin ayyukan jin kai.
Jacob Zocherman/Merlin
Ms Kpakanale ta haifi da namiji a ranar 17 ga watan Yuli, kuma an yiwa danta allurar riga kafi a asibitin Obo.