BBC navigation

Ayyukan kashe gobara a kasar Saliyo

An sabunta: 10 ga Yuli, 2013 - An wallafa a 13:31 GMT

'Yam kwana-kwana na Freetown

 • Wata ma'aikaciya na jiran kiran daukin gaggawa
  Esther Magati na jiran kiran neman daukin gaggawa a babban ofishin 'yan kwana-kwana dake Freetown, babban birnin Saliyo. Mutane dai na iya kiran ofishin ne kawai idan suna amfani da layin waya na Africell, yayin da sauran ana tura wayoyinsu zuwa garin Mile 91 dake gabashin birnin.
 • Ruwa na diga daga mesar ruwa. Hoto: Tommy Trenchard
  Hakazalika rundunar ta 'yan kwana-kwana tana fuskantar matsalar karancin ruwa da ma mesar ruwa. A lokacin da ruwan tankin motar kashe gobara ya kare, sai an yi tafiya mai nisa kafin a sake cika tankin, sannan a koma domin kashe gobarar.
 • Masu kashe gobara na baiwa ciyayi ruwa, a kofar Fadar Shugaban Kasa
  Duk da karancin ruwan da suke fama da shi, sauran ayyukan da 'yan kwana-kwanan suke yi sun hada da kula da farfajiyar Fadar Shugaban Kasa, gabannin tarurruka.
 • Gidajen kwano. Hoto: Tommy Trenchard
  Babban jami'in kashe gobara Naziru Bongay ya ce: "Kashi 60 cikin dari na gidaje an rufa su ne da kwano, da itatuwa, da kuma kwalaye. Kuma idan ka kalli wadanan kayayyakin gini, muna kiransu gidaje marsa nagarta, ba su da wuyar kama wuta."
 • Wayoyin wutar lantarki a bude a babban ofishin 'yan kwana-kwana
  Ana yawan samun gobara ta dalilin wutar lantarki a Saliyo, inda cakuda wayoyin lantarki, da karuwar/raguwar karfin wuta, da kuma lodi fiye da kima ke haifar da barazanar aukuwar gobara.
 • Gidaje marasa nagarta. Tommy Trenchard
  Yanayin kasa da cunkoso ma kalubale ne a Freetown. A cewar Mista Bongay, "Wadansu wuraren tuddai ne, ga gabar ruwa; ga wadansu wuraren babu tituna. Saboda haka a duk lokacin da aka samu gobara ana samun kalubale kwarai."
 • Motar kwana-kwanan da ta lalace. Tommy Trenchard
  A lokacin bazarar da ya wuce, 'yan kwana-kwanan sun karade kusan fadin birnin Freetown, birnin dake da mutane fiye da miliyan daya, da motar kashe gobara guda daya, bayan sauran guda biyun da suke da su sun lalace. "Ba abu ne mai sauki ba", inji babban jami'in kashe gobarar.
 • Wasu suna motsa jiki kafin fara wasan kwallo
  Jami'in kashe gobara Mohammed S Kamar na shirin wasan kwallo a filin dake bayan ofishin 'yan kwana-kwanan. Kasancewa cikin koshin lafiya a cewarsa yana da muhimmanci a irin aikin da yake yi.
 • Wani dan kwana-kwana yana kashe gobara. Tommy Trenchard
  Santigi Bangura na kashe wata wuta da ta tashi a sanadiyyar lalacewar na'urar lantarki a Freetown, lamarin da ya yi sandiyyar mutuwar mutum guda. Duk da cewa sinadarai na tashi a lokacin ayyukansu, amma haka jami'an suke aiki ba tare da abin kare numfashinsu ba. "Idan da suna da kayan aiki masu inganci hakan zai fi, amma kwarin gwiwa da zummar da suke da shi ga aikin--su ma suna da muhimmanci," inji Mista Bongay.
 • Dan sanda na kokarin kwantar da wata 'yar karamar tarzoma da ta barke saboda 'yan kwana-kwana ba su kai dauki da wuri ba. Tommy Trenchard
  A wasu lokuta ma'aiakatan kwana-kwanan na fuskantar cin zarafi. Idan mutane suka ga cewa ba su zo da wuri ba, a kan kai musu hari, abin da kan sa su koma kafin ma su kai ga kashe wutar dake ci.
 • Mulk Sulaiman na zaune a kofar gidan abokin aikinsa
  Mulk Sulaiman na zaune a kofar gidan wani abokin aikinsa, daura da ofishin 'yan kwana-kwanan, bayan kammala wani horo. Tun lokacin da ya ke da kuruciya abin da yake fatan zama shi ne ya zama jami'in kashe gobara.
 • Maliki S. Kamara a kofar ofishin 'yan kwana-kwana. Tommy Trenchard
  Maliki S. Kamara ya fara aikin kashe gobara a shekarar 1975 kuma an sanya masa suna "Jami'in kashe gobara mafi kokari a Freetown." Mista Kamara ya kashe daruruwan gobara kuma shi ne mutum na farko dake fara shiga ginin dake cin wuta. Abin fata a yanzu shi ne a samu masu gadonsa a tsakanin al'umma masu tasowa. Tommy Trenchard ne ya dauki duka hotunan.

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.