Ra'ayi Riga: Tasirin Fina-finan Bollywood

3 Mayu 2013 An sabunta 23:17 GMT

Amitabh Bachan
Amitabh Bachan

Tun a shekarar 1913 ne masana'antar fina-finan india wadda ake kira Bollywood ta fara yin fina finan da ake kallo a sinima a kasar.

Kuma sannu a hankali masana'antar ta rika bunkasa har ta kai tana fitar fina finanta kasashen waje, cikin kuwa har da kasashen Afurka.

Najeriya ta kasance wata babbar kasuwar fina-finan india, inda gabanin zuwan akwatinan talabijin kasar, akan nuna fina finan ne a gidajan silima.