BBC navigation

Hotuna: Zaben kasar Kenya

An sabunta: 4 ga Maris, 2013 - An wallafa a 14:21 GMT

Hotuna: Zaben kasar Kenya

 • Hotuna: Zaben kasar Kenya
  Jama'ar kasar Kenya na kada kuri'a a zaben da masu sanya ido suka bayyana da cewa shi ne mafi mahimmanci a tarihin kasar.
 • Hotuna: Zaben kasar Kenya
  An tsara sabon kundin tsarin mulki domin kaucewa tashin hankalin da aka fuskanta a shekara ta 2007.
 • Hotuna: Zaben kasar Kenya
  Manyan 'yan takarar shugabancin kasar Fira minista Raila Odinda da Uhuru Kenya suna tafiya kafa-da-kafa. Uhuru kenan yake kada kuri'a a nan
 • Hotuna: Zaben kasar Kenya
  Jama'a sun fara kafa dogayen layuka tun da sanyin safiya a sassa daban daban na kasar domin ganin sun kada kuri'arsu
 • Hotuna: Zaben kasar Kenya
  Al'ummar Kenya za su zabi, 'yan majalisa da gwamnonin lardi da kuma yan majalisun lardi.
 • Hotuna: Zaben kasar Kenya
  'Yan takarar na bukatar samun goyon baya daga dukkan jama'ar kasar saboda kada su dogara da goyon bayan da suka samu daga kabilunsu
 • Hotuna: Zaben kasar Kenya
  Duk da cewa dai an yi gangamin neman zaman lafiya, rahotanni sun ce an kashe jami'an 'yan sanda biyu a kusa da Mombasa da safiyar ranar Litinin.
 • Hotuna: Zaben kasar Kenya
  Akalla mutane shida - ciki harda maharan - aka bada rahoton sun mutu a harin na Changamwe, mai nisan sa'a guda daga tsakiyar garin Mombasa.

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.