Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Mutum-mutumin dorinar ruwa na gasar cin kofin Afrika

6 Fabrairu 2013 An sabunta 15:02 GMT

Gasar wasannin kwallon kafa na nahiyar Afirka
Gasar wasannin kwallon kafa na nahiyar Afirka

Wani abin da ya ja hankali a gasar cin kofin nahiyar Afrika, da ake yi a Afirka ta Kudu shi ne batun Takuma, wani mutum-mutumin dorinar ruwa.

Sai dai abin da ba lallai bane mutane su sani ba shi ne, wani yaro maraya dan shekara 13 mai suna Tumela Nkoana ne ya zana shi.

Yaron na zaune ne a wani karamin gari a arewacin Afirka ta kudu wato Hammanskreal.