BBC navigation

Ra'ayi Riga:Shirin rarraba wayoyin salula ga manoma a Najeriya

An sabunta: 11 ga Janairu, 2013 - An wallafa a 21:08 GMT

Garmaho

Gwamnatin Najeriya ta ce za ta bullo da shiri na rarraba wayoyin salula kyauta ga manoma miliyon goma, ta yadda za su samu saukin samun muhimman bayanai kan sana'arsu. Ko mecece fa'idar shirin? Ta yaya manoman za su ci gajiyar shirin?

Sauraremp3

Ba ka da manhajar flash player da ta dace

Kunna wannan da wata manhajar ta daban

Wani manomi a Najeriya

Yawancin manoma a Najeriya na amfani da dabarun gargajiya ne a sana'arsu

A Najeriya, a farkon watan nan ne aka ambaci babban sakataren ma'aikatar ayyukan noma ta kasa, Ibukun Odusote yana cewar gwamnatin kasar ta kammala wani shiri na samar da wayar salula kyauta ga manoma miliyan goma a yankuna karkara.


Mr Odusote ya ce hakan zai ba ma'aikatarsu damar ilmantar da manoman da kuma tuntubar su, duk dai a yunkurin bullo da zamananci a ayyukan noman a Nijeriya.


To sai dai shirin na shan suka daga bangarori da dama, inda wasu ke korafin cewa ba abin da manoman karkara suka fi bukata ba kenan.

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.