BBC navigation

Ra'ayi Riga:Najeriya ta taka rawar gani a gasar Olympics ta nakasassu

An sabunta: 7 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 20:39 GMT

Garmaho

'Yan wasan Najeriya wadanda suka halarci gasar Olympics ta nakasassu wato Paralympics sun taka rawar gani a gasar, amma takwarorinsu da suka halarci gasar Olympics ba suyi abin azo agani ba.

Sauraremp3

Ba ka da manhajar flash player da ta dace

Kunna wannan da wata manhajar ta daban

olympics

Dan wasan Najeriya wasan wanda ya lashe zinare a gasar Paralympics

A 1992 ne Najeriya ta fara shiga gasar wasannin Olympics ta nakasassu, wato Paralympic a birnin Barcelona na Spain.

A lokacin dai ta tura 'yan wasa maza ne guda shidda, domin shiga wasannin guje guje da tsalle da daga nauyi da kuma kwallon tebur.

A wannan gasar dai Nijeriyar ta samu lambobin yabo na gwal guda uku, biyu a gudu daya a daga nauyi.

Tun daga lokacin, Najeriya ba ta taba fashin shiga gasar ba.

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.