'Yan wasan kwallon Afirka a Gasar Premier
-
Dan wasan tsakiya na Ivory Coast, Yaya Toure (a shudiyar riga), zai sake zama zakaran gwajin dafi a Manchester City a yunkurinsu na sake lashe Gasar Premier. Kasancewar Yaya a kungiyar ta Manchester City ta taka muhimmiyar rawa a kakar bara, sannan kuma ya jefa kwallaye masu zafi a raga - ga alama kuma za a ci gaba da ganin hakan idan aka yi la'akari da rawar da ya taka a nasarar da suka yi a kan Chelsea da ci uku da biyu a wasan cin Garkuwar Community Shield.
-
Hakazalika Manchester City din na da dan wasa mai tashe, wato Abdul Razak (a shudiyar riga), wanda karansa zai iya kai tsaiko mamaki bana. Tuni dan wasan na tsakiya mai shekaru 19 da haihuwa ya samu gurbi a tawagar Ivory Coast kuma zai zaku ya ya ci gaba da takawa City leda bayan ya kuskurewa fitowa a wasan cin Garkuwar Community Shield.
-
Wigan ta samo dan wasan gaba na Ivory Coast Arouna Kone (a gefen hagu) wanda ya ce saboda falsafar kwallo ta kocin Wigan Roberto Martinez da salon wasanta ya shiga kungiyar. Kone, dan shekara 28, ya koma Wigan ne daga kungiyar Levante ta Spain, inda ya ci kwallaye 15 a wasanni 34 a kakar wasanni ta bara.
-
Haka nan kuma kungiyar ta Wigan ta dauko wani hazikin da wasan Afirka, wato Modibo Maiga, wanda ke bugawa tawagar Mali wasan gaba ko na gefe. Ya dawo kungiyar ta gabashin London ne daga Sochaux. Saboda matsuwar da ya yi ya bar fagen gasar Faransa har yajin aiki ya yi a kakar wasa ta bara don tilastawa kungiyar ta kyale shi ya tafi Newcastle.
-
Victor Moses ma (a gefen dama) wani tauraron dan wsa ne na Afirka a Gasar Premier, ko da yake har yanzu ba shi da tabbas a kan Wigan zai takawa leda ko Chelsea, kungiyar da ke kokarin sayen shi daga Latics. Dan wasan mai dan karen gudu ya bugawa Ingila a matakin 'yan kasa da shekaru 21 amma ya zabi bugawa Najeriya a matakin manya, kuma sau uku yana takawa Super Eagles leda.
-
A watan Janairu Papis Cisse ya shiga sahun 'yan wasan Newcastle kuma dan wasan na Senegal bai bata lokaci ba ya zama dan gida, har ma ya ci kwallaye 13 a wasanni 14. A kakar wasa ta bara kungiyar ta Newcastle ta kare ne a matsayi na shida a teburin Premier kuma za ta bukaci Cisse ya yi wuta kamar bara in har tana so ta kwata hakan.
-
Kakar wasa ta bara ce ta fi kowacce ga Alex Song a Arsenal, lokacin da ya dauki hankalin 'yan kallo da yadda yake gyara kwallo da kuma zalakarsa ta tsaron baya. Sai dai nan ba da jimawa ba dan wasan na Kamaru zai bar Gasar Premier ya koma ta La Liga-- Barcelona ta nuna sha'awar sayen dan wasan mai shekaru 24.







































