A Hyderabad, in ba ka dandana haleem ba, ba ka yi bude-baki ba
-
A lokacin azumin watan Ramadan, bude-bakin mutanen Hyderabad ba ya kammala ba tare da Haleem ba, wani abinci mai kauri kamar talge (ko dan malele) da ke da dadi. Ana yinsa ne da alkama, da shinkafa, da nama, ana kuma tsarma kayan yaji, da busassun 'ya'yan itace da sauran abubuwa. Iraniyawa ne suka kawo haleem birnin Hyderabad mai shekaru 400.





































