bbc.co.uk navigation

Yunkurin kallon Olympic a titunan Landan

An sabunta: 10 ga Agusta, 2012 - An wallafa a 15:10 GMT

Yunkurin kallon Olympic a titunan Landan

  • Hotuna: Omid Salehi
    Dubbban jama'a ne suke taruwa a dandalin shakatawa na Hyde Park da ke tsakiyar birnin Landan domin kallon wasannin Olympics.
  • Hotuna: Omid Salehi
    Mutanen da ke kallon gasar a manyan allunan talabijin a dandalin Hyde Park - wasunsu na zaune ne a kan burbushin katako.
  • Hotuna: Omid Salehi
    Wasu mutanen sun fi son su kalli wasannin a dandali maimakon gidajensu
  • Hotuna: Omid Salehi
    Kuma sukan kasance cikin nishadi da murna idan kasar da suke goyon baya ta samu nasara
  • Hotuna: Omid Salehi
    Wasu daga cikin shahararun 'yan wasan na Olympics kan ziyarci jama'ar gari a dandalin na Hyde Park
  • Hotuna: Omid Salehi
    A lokacin hutu, masu kade-kade da raye-raye kan nishadantar da 'yan kallo
  • Hotuna: Omid Salehi
    Ana iya kuma ganin wasu masu raye-raye a kan titunan birnin na Landan
  • Hotuna: Omid Salehi
    Wasu 'yan Gabashin Asia na taka rawa a daya daga cikin titunan Landan
  • Hotuna: Omid Salehi
    A lokacin wasannin, ana iya ganin jama'a da dama suna sanya kaya masu laurin tutar Burtaniya
  • Hotuna: Omid Salehi
    A kowacce rana ana iya ganin tawagar wata kasa sanye da kayayyakinsu na gargajiya
  • Hotuna: Omid Salehi
    'Yan yawon bude ido kan taru a kowanne dare a Piccadilly Circus da ke tsakiyar birnin London domin kallon wasannin a babban allon talabijin
  • Hotuna: Omid Salehi
    Wannan shi ne irin babban allon da jama'a ke kallon gasar a jiki
  • Hotuna: Omid Salehi
    Duk inda ka zagaya a birnin za ka ga alamar gasar ta Olympic

BBC © 2013 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.