-
Wannan bangaren da za a gudanar da wasan kwallon kwando na daya daga cikin filaye mafiya girma da aka gabatar da wasannin Olympics. Mutane 12,000 za su iya haduwa a wannan filin. Kuma za a iya gudanar da wasannin Olympic da na nakasassu da ake kira 'Paralympic', filin zai kuma karbi bakuncin wasan kwallon kwando.
-
Daga hagu: Filin wasa na Wembley zai dauki bakuncin gasar kwallon kafa a yayin da a Wembley Arena za a yi wasannin badminton da rhythmic gymnastics, Excel - boxing, fencing, judo, table tennis, taekwondo, weightlifting da kuma dambe; sai filin North Greenwich Arena - inda za a yi gymnastics, trampoline da kwallon kwando.
-
Cibiyar Lee Valley White Water da ke Hertfordshire nan ne waje na farko da aka kammala don gasar Olympics tun a watan Disambar 2010. Masu tseren jirgin ruwa su ne za su kasance a wajen. Sai kuma wasu masu tseren da za su yi a Weymouth da Portland da ke Dorset, inda anan za a ga wajen tarihi a Burtaniya. Kuma a halin yanzu ana ci gaba da bunkasa wajen.
-
Za a soma gasar London 2012 a Cardiff da kwallon kafa na mata a ranar 25 ga watan Yuli wato kwanaki biyu kafin bukin bude gasar. Za a yi amfani da filayen kwallon kafa a Burtaniya lokacin gasar. Daga hagu: Hampden Park, Glasgow; St James' Park, Newcastle; City of Coventry Stadium; Wembley, London; Millennium Stadium, Cardiff and Old Trafford, Manchester.


















