BBC navigation

Hotuna: Zaben shugaban kasa a Masar

An sabunta: 23 ga Mayu, 2012 - An wallafa a 13:38 GMT

Hotuna: Zaben shugaban kasa a Masar

 • Hotuna: Zaben shugaban kasa a Masar
  Miliyoyin masu kada kuri'a ne suka fara kada kuri'a a kasar Masar, domin zaben sabon shugaban kasar, wanda ake ganin shi zai kasance sahihin zaben shugaban kasar a karon farko cikin tarihi.
 • Hotuna: Zaben shugaban kasa a Masar
  Wakilin BBC a Alkahira babban birnin kasar, ya ce tunda sanyin safiya jama'a suka fara fita domin yin dogayen layuka - abinda ke nuna aniyarsu ta kada kuri'a a zaben.
 • Hotuna: Zaben shugaban kasa a Masar
  'Yan takara goma sha biyu ne ke fafatawa a zaben da za a shafe kwanaki biyu ana yi kuma ana sa ran masu kada kuri'a miliyan 50 ne za su yi zabe.
 • Hotuna: Zaben shugaban kasa a Masar
  A karon farko cikin tarihin kasar da ya zarta shekaru dubu biyar, sun samu damar zaben shugaban kasar su ba tare da tursasa wa ba.
 • Hotuna: Zaben shugaban kasa a Masar
  Mutane hudun da ake ganin su ne na gaba-gaba a zaben, ko dai masu kishin addinin Musulunci ne ko kuma tofaffin ministoci da suka rike mukami a gwamnatin da ta shude.
 • Hotuna: Zaben shugaban kasa a Masar
  Wani jami'in sojin kasar Masar yana taimakawa wani tsoho a birnin Alkahira, domin ya samu damar kada kuri'a a zaben shugaban kasar mai cike da tarihi.
 • Hotuna: Zaben shugaban kasa a Masar
  Idan ba a samu dan takara daya da ya yi zarra ba, to 'yan takara biyu da suka fi samu kuri'a za su je zagaye na biyu
 • Hotuna: Zaben shugaban kasa a Masar
  An girke jami'an tsaro a sassan kasar da dama domin tunkarar duk wani tashin hankali da ka iya afkuwa a lokutan zaben.
 • Hotuna: Zaben shugaban kasa a Masar
  An dai samu tashin hankula a 'yan kwanakin nan tsakanin masu adawa zanga-zangar da mulkin soji da kuma jami'an tsaro, wanda hakan ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama.

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.