BBC navigation

Hotuna: Yadda rayuwa ta ke a nahiyar Afrika

An sabunta: 27 ga Aprilu, 2012 - An wallafa a 20:04 GMT

Hotuna: Yadda rayuwa ta ke a nahiyar Afrika

 • Hotuna: Yadda rayuwa ta ke a nahiyar Afrika
  Ana yiwa nahiyar Afrika kallo ta fuska daban-daban a duniya, daga batun yunwa, talauci sai yake-yake. Mai zane-zane Jepchumba na Kenya ne ya shirya wadannan hotunan, domin su dace da shirin BBC na Africa Debate wanda ya tattauna a kan yadda ake kallon nahiyar Afrika a duniya.
 • Hotuna: Yadda rayuwa ta ke a nahiyar Afrika
  Glenna Gordon, 'yar kasar Amurka ta shafe dogon lokaci tana daukar hotuna a kasar Liberia da kuma Yammacin Afrika. Ta gano yadda cewa son zuciya yana tasiri a harkokin rayuwa a nahiyar.
 • Hotuna: Yadda rayuwa ta ke a nahiyar Afrika
  Daya daga cikin yadda ake kallon rabe-raben nahiyar Afrika shi ne batun mulkin mallaka, amma har yanzu nahiyar na janyo hankalin jama'a daga kasashen waje. © Giulia Marchi
 • Hotuna: Yadda rayuwa ta ke a nahiyar Afrika
  Yawancin hotunan sun nuna yadda Afrika ta ke da dazuka da fadin kasa. Sai dai biranen Afrika na ci gaba da bunkasa. © Jide Alakija
 • Hotuna: Yadda rayuwa ta ke a nahiyar Afrika
  Kama daga birnin Nairobi zuwa Cape Town, akwai damarmaki na kasuwanci duk da matsalar tattalin arziki da rayuwar yau da kullum da ake fuskanta. © Dillon Marsh
 • Hotuna: Yadda rayuwa ta ke a nahiyar Afrika
  Wannan birnin Nairobi na kasar Kenya kenan cikin dare. Shida daga cikin kasashen Afrika na daga cikin kasashe 10 da suke bunksa cikin gaggawa hatta ta fuskar fasaha. Wannan yana tasiri wurin bunkasar biranen nahiyar. © Mutua Matheka
 • Hotuna: Yadda rayuwa ta ke a nahiyar Afrika
  Kamar sauran biranen Afrika, birnin Alkahira ya hada da gine-ginen tarihi da kuma na zamani. © Alberto Cassani
 • Hotuna: Yadda rayuwa ta ke a nahiyar Afrika
  Ganin yadda Afrika ta ke yawan matasa a duniya, yawancin birane kamar Soweto na Afrika ta Kudu, na kirkiro sabbin hanyoyi kamar na wakoki da dinke-dinke da kuma al'adu. © I See a Different You
 • Hotuna: Yadda rayuwa ta ke a nahiyar Afrika
  'Yan Afrika na shiga ana fafatawa da su a fagen internet da shafukan sada zumunta na duniya kamar Facebook da Twitter da sauransu. © Jide Alakija

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.