BBC navigation

Bala'in yankin Sahel na Afirka ta Yamma a hotuna

An sabunta: 29 ga Maris, 2012 - An wallafa a 17:44 GMT

Bala'in yankin sahel a cikin hotuna

 • Aboubacar da matarsa Maryama, daga kauyen Kadago Biri a Nijar
  Kungiyoyin agaji sun yi gargadin cewa farin da ake fama da shi a yankin Sahel na Yammacin Afirka zai iya zama wata babbar annoba. Tamowa da ma sauran cututtuka sun jefa rayukan dubban mutane cikin hadari a Chadi, da Burkina Faso, da Mali, da Mauritania, da Nijar, da arewacin Senegal. Kungiyar agaji ta liktoci, wato Doctors Without Borders/Médecins Sans Frontières (MSF) ce ta dauki wadannan hotunan.
 • Aboubacar da diyarsa Aicha
  Aboubacar, daga kauyen Kadago Biri a Nijar, ya kai 'yarsa Aicha—wacce ke fama da kumburin ciki—wani wurin shan magani na kungiyar MSF. A can ne ya samu labarin cewa matarsa Maryama, wacce ka da juna-biyu, ta yi bari kuma tana can rai-kwakwai-mutu-kwakwai. Cikin ikon Allah Maryama da Aicha sun samu lafiya.
 • Wani gida a kauyen Kadago Biri a Nijar
  Kungiyar MSF ta ce a kauyukan Nijar, ga akasarin mutane ganin likita sai wane-da-wane. Saboda nisan cibiyoyin kula da lafiya da karancin ababen hawa da rashin kyawun hanyoyi, uwaye da yara da dama ba sa isa asibitoci a kan lokaci.
 • Dabbobi
  Ba mutane ne kawai ke shan wahala ba sakamakon fari a yankin. Dabbobinsu ma sun fada halin ha'ula'i sakamakon karancin ruwa da ciyawa ko harawa.
 • Wata rijiya a wani kauye.
  A wadansu lokutan a kan rasa isasshen ruwan da zai gamsar da jama'a a rijiyoyin da ke kauyukansu, ballantana dabbobinsu su samu.
 • Wani sansanin 'yan gudun hijira na Hukumar Kula da 'Yan Gudun Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya a garin Abala da ke Nijar
  Wata karin matsala a Nijar ita ce kwararowar 'yan gudun hijira daga Mali, mai makwabtaka, a 'yan watannin da suka gabata.
 • 'Yan gudun hijirar Mali a Nijar
  Mutane da dama na tserewa daga rikicin da ke aukuwa a arewacin Mali, hakan kuma na nufin an yiwa albarkatun Nijar, wadanda da ma ba su taka kara sun karya ba, yawa.
 • Yara a Nijar.
  Cibiyoyi da dama sun kaddamar da gidauniyar neman taimakon gaggawa don tara miliyoyin daloli da nufin taimakawa wadanda suka fi galabaita. A cewar Daraktan Yanki na Afirka ta Yamma na kungiyar Oxfam, Mamadou Biteye, "Dukkan alamu na nuna cewa farin zai zama wata babbar annoba idan hanzarta daukar mataki ba. An samo wannan hoton ne daga kungiyar Oxfam
 • Bengali Tani
  Sai dai kuma cibiyoyin sun kwan da sanin cewa ana bukatar a kara zage dantse don karfafawa al'ummar yankin gwiwa su daina dogaro da kayan agaji. Wannan matar auren 'yar shekara 40, Bengali Tani, tana da 'ya'ya goma, kuma daya ce daga cikin wadanda suka amfana da wani shiri na Oxfam a Nijar, inda mutane ke aiki ana biyansu. An samu wannan hoton ne daga Oxfam
 • Mutane suna tara kasa
  Ana biyan Malama Tani da mutanen kauyensu da dama su tara kasa ta yi kamar tsayuwar wata saboda ta tare ruwan sama lokacin damuna mai zuwa. Ana fatan hakan zai taimaka wajen kara yawan ruwan da ke kasa, ya kuma tallafawa shuke-shuke da gonaki farfadowa. An samu wannan hoton ne daga Oxfam

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.