BBC navigation

Bidiyon koyar da wariyar launin fata a Afrika ta kudu

An sabunta: 20 ga Maris, 2012 - An wallafa a 16:09 GMT

Hotuna: Bidiyon koyar da wariyar launin fata

  • Hoton bidiyo mai firgitarwa na Afrikaner Blood wanda Elles Van Gelder da kuma IIvy Njiokiktjien 'yan kasar Netherlands suka dauka ya zo na daya a gasar daukar hotuna ta kungiyar 'yan jaridu ta duniya.
  • Acewar wadanda suka shirya shirin bidiyon, wani gungun da ba su yi suna ba, Kommandokorps na koyar da wasu da ake kira, Afrikaner boys yadda za su ki amincewa da burin Nelson Mandela na rashin nuna wariyar launin fata.
  • "Yaran dake cewa sun amince a daina nuna wariyar launin fata kuma suna da abokai bakaken fata 'yan Afrika ta kudu, ana hure musu kunne a sansanin. Da zarar sun bar sansanin sam ba sa son ace musu 'yan Afrika ta kudu, sannan sunyi amanna cewa bakake 'yan Afrika ta kudu abokan gabarsu ne." Inji Ms. Van Gelda.
  • Franz Jooste(na tsakiya) shi ne jagoran kungiyar, kuma soja ne a lokacin mulkin tsiraru fararen fatan da ya kawo karshe a shekarar 1994, bayan zaben Nelson Mandela a matsayin shugaban kasar bakin fata na farko.
  • "Ba na jin kunyar nuna wariyar launin fata. A Afrika ta kudu dayan biyu ne, ko ka rufe ido kamar ba ka san abinda ake ciki ba ko kuma ka zama mai nuna wariyar launin fata." Inji Jooste. Bayan kwashe shekaru ana nuna bangaranci na launin fata, bakake da fararen fata a Afrika ta kudu suna hulda ba tare da wata matsala ba. Sai dai fararen fatan na kokawa game da yawan kisan fararen fata, musamman manoma. Haka kuma wasu bakaken fata na korafin cewa ana cigaba da nuna musu wariya ta fuskar tattalin arziki.
  • Acewar Ms. Van Gelder, Mr. Jooste na cigaba da kasancewa cikin duhun abinda ya faru a baya. Bai yi amanna da nuna wariyar launin fata ba, amma yana da ra'ayin cewa yakamata fararen fata su samu kasar su ta daban, kuma ba za su zauna tare da bakaken fata ba, don ba daya suke ba.
  • "Mu Afrikaners mutane ne masu radin kansu. Wannan abinda mu keyi na nuni da rashin mutunta wannan abin." Inji Tsohon sojan, yayinda hoton bidiyon ke nuna wasu yara na tattaka tutar Afrika ta kudu.
  • "Ya dauke ni sa'a daya kacal wajen sauya ra'ayinsa. Daga nan ya gane cewa shi ba dan Afrika ta kudu ba ne. Dan wata kasa ne daban mai alfahari da tarihinta." Mr. Jooste na cika baki. Kungiyar Kommandokorps na ikirarin horar da mutane 1500 daga cikin fafaren fata miliyan 4.6 dake Afrika ta kudu.
  • Riaan wani dan shekaru 18 ne kuma yace: " Kasar Afrika ta Kudu ana ce mata kasar bakan-gizo ne saboda akwai kabilu da dama a cikinta." Sai dai bayan samun horon ra'ayinsa ya sauya. " Ina da jinin Afrikaner a jikina. Ba na son zama dan Afrika ta kudu, kuma ba na son wani abu ya hada ni da kasar bakan-gizo.
  • Lucy Holborn ta SAIRR ta ce bidiyon ya firgita mutane da dama. Amma bai dau wani lokaci ba, hakan yayi sauki da mutane suka fahimci cewa ana maganar mutane kalilan ne cikin fareren fatar dake kasar.

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.