bbc.co.uk navigation

Hotuna: Zanga-zangar adawa da Amurka a Afghanistan

An sabunta: 22 ga Fabrairu, 2012 - An wallafa a 12:19 GMT

Hotuna: Zanga-zangar adawa da Amurka a Afghanistan

  • Zanga-zangar adawa da Amurka a Afghanistan
    Jama'a na ci gaba da zanga-zangar nuna kin jinin Amurka, bayan da sojojin Amurka da ke sansanin Bagram suka kona wasu takardu ciki harda Alkur'ani.
  • Zanga-zangar adawa da Amurka a Afghanistan
    Zanga-zangar na kara munana ce duk da kwamandan Amurka a kasar Janar Allen ya nemi afuwa kan abinda ya faru, sannan ya yi alkawarin gudanar da cikakken bincike.
  • Zanga-zangar adawa da Amurka a Afghanistan
    'Yan sanda sun shaida wa BBC cewa akalla mutane 1,000 ne suka shiga zanga-zangar a ranar Litinin, yayin da wasu dattawan yankin suka shiga sansanin domin tattaunawa da dakarun Nato.
  • Zanga-zangar adawa da Amurka a Afghanistan
    Jami'an Afghanistan sun shaida wa kamfanin dillancin labarai na AP cewa, an ga Alkur'ani a wata shara da wasu sojojin Amurka biyu suka kai wurin da ake kona bola ranar Litinin da daddare.
  • Zanga-zangar adawa da Amurka a Afghanistan
    Lokacin da 'yan Afghanistan biyu da ke aiki a wurin suka gano Alkur'anin, sai suka dakatar da shirin zubar da sharar.
  • Zanga-zangar adawa da Amurka a Afghanistan
    Wani wakilin BBC a wurin ya ce ya ga mutane suna kuka kan zargin cewa dakarun kasashen waje sun kona Al'kur'ani, yayin da wasu ke jifan dakarun tsaro da duwatsu.
  • Zanga-zangar adawa da Amurka a Afghanistan
    Rahotanni sun ce masu gadi a wurin sun yi amfani da harsashen roba kan masu zanga-zangar da ke kiran "Allahu akbar, Allahu akbar".
  • Zanga-zangar adawa da Amurka a Afghanistan
    A sanarwar da ya fitar, Janaral Allen ya ce binciken zai gano ko sojoji a Bagram "sun zubar da takardu da suka hada da Alkur'ani ta hanyar da bata dace ba".
  • Zanga-zangar adawa da Amurka a Afghanistan
    "Muna gudanar da cikakken bincike, domin tabbatar da cewa hakan bai kara faruwa a nan gaba ba. Ina baku tabbaci....Na yi muku alkawari...wannan ko kadan bai dace da halayyar kasashen duniya ba."

BBC © 2012 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.