bbc.co.uk navigation

Kididdiga: Talauci ya karu a Najeriya

An sabunta: 17 ga Fabrairu, 2012 - An wallafa a 23:01 GMT

Garmaho

A wani rohoton da ta fitar, Hukumar Kididdiga ta Kasa a Najeriya ta ce talauci ya karu idan aka kwatanta da shekarar 2004.

Sauraremp3

Ba ka da manhajar flash player da ta dace

Kunna wannan da wata manhajar ta daban

Matalauta a Jihar Sokoto, Najeriya

Matalauta a Jihar Sokoto, Najeriya

A wani rohoton da ta fitar a farkon makon nan, Hukumar Kididdiga ta Kasa a Najeriya (National Bureau for Statistics) ta ce talauci ya karu a kasar idan aka kwatanta da shekara ta 2004.

Hukumar ta bayyana cewa fiye da kashi sittin cikin dari na 'yan kasar ne ke rayuwa a kasa da kwatankwacin dalar Amurka daya a kowacce rana, wato mutane kusan miliyan dari ke nan, daga cikin dukkan 'yan kasar kusan miliyan dari da 60.

Rahoton ya kuma ce a yankin arewacin kasar ne talaucin ya fi kamari.

Hukumar ta ce amfani da kiddigar zai iya taimakawa gwamnatoci su yi gyare-gyare a kan abubuwan da suka shafi ci gaba.

Wannan ne batun da muka tattauna a kai a shirin Ra'ayi Riga na wannan makon.

BBC © 2012 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.