bbc.co.uk navigation

Hotuna: Tasirin man fetur a kasar Equatorial Guinea

An sabunta: 14 ga Fabrairu, 2012 - An wallafa a 16:45 GMT

Hotuna: Tasirin man fetur a kasar Equatorial Guinea

  • Filin wasan kwallon kafa na Malabo
    A makonnin da suka wuce ne Equatorial Guinea ta karbi bakuncin gasar cin kofin kwallon kafa ta kasashen Afrika tare da Gabon. Wakilin BBC Manuel Toledo ya dauko hotuna bayan da ya kai ziyara kasar a 'yan kwanakin nan.
  • Paseo Maritimo, Bata
    Equatorial Guinea na ci gaba da bunkasa cikin gaggawa tun bayan fara hako man fetur a shekarun 1990. Gwamnati na da wani shiri da ta kira Horizon 2020, da nufin shigar da kasar sahun kasashe masu tasowa cikin shekaru takwas masu zuwa. Nan wani bangare ne na Bata, birni mafi muhimmanci a kasar.
  • Dandalin Cathedral na Malabo
    Amma a lokaci guda, mutane a kasar na cewa an rusa gine-gine masu kyau da dama da sunan kayata birnin. Dandalin cathedral da ke Malabo babban birnin kasar, na dauke da wasu gine-ginen tarihi na lokacin mulkin mallaka amma yanzu an maye gurbinsu da ofisoshin gwamnati na zamani.
  • Birnin Malabo
    Kasar Equatorial Guinea wacce ke kusa da gabar kogin tsakiyar Afrika, ta samu 'yancin kai ne daga Spain a 1968. Birnin malabo ya samu sunansa ne a 1973 domin martaba sarkin kabilar Bubi.
  • 'Yan kabilar Bubi a Cibiyar raya al'adun Spain
    Wadannan mutanen kabilar Bubi ne daga Moka, wani kauye a Bioko. Ana amfani da harsunan Spaniyanci da Faransanci a Hukumance a kasar, yayin da harsunan Fang da Pichi ke kan gaba a harsunan cikin gida.
  • Hotunan neman daidaito a Malabo
    Akwai hotuna makamantan wannan da dama a kasar da ke kira da a samar da daidaito tsakanin jinsi. Daya daga cikin shahararrun mawakan kasar Yuma, ta yi wata waka mai suna "Victim" inda ta soki dabi'ar cin zarafin mata.
  • Hoton  shugaba Teodoro Obiang Nguema
    Akwai hotunan shugaba Teodoro Obiang Nguema Mbasogo a wurare da dama. An zarge shi da take hakkin bil'adama, zargin da ya sha musantawa.
  • Birnin Bata
    Mr Obiang ya hau kan mulki a shekarar 1979, lokacin da ya yiwa dan uwansa Francisco Macias Nguema juyin mulki. Shi ma dai an zarge shi da mulkin kama-karya.
  • Hoton nuna goyon baya ga sauyin tsarin mulki
    A bara aka sauya kundin tsarin mulkin kasar domin takaita wa'adin shugaban kasa zuwa karo biyu. Ana yiwa matakin kallon wani zakaran gwajin dafi ta fuskar demokuradiyya ga Mr Obiang.
  • Gidaje a birnin Bata
    Babu jaridar da ake wallafawa kowacce rana a kasar, amma mutane da dama na samun damar kallon talabijin ta tauraron dan adam da kuma internet. A birnin Malabo, ana sake watsa shirin gidan rediyon BBC na Turanci a gidajen rediyon FM.
  • Tsakiyar birnin Bata
    Yawancin matasan da BBC ta yi magana da su a sassan kasar da dama na da fata nagari ga makomar kasar, sabanin yadda ake hasashe a kasashen waje cewa mutane kalilan ne ke amfana da arzikin man kasar.
  • Mai zane  Luis Royo del Pozo
    Wannan zanen na Luis Royo del Pozo na nuna yadda birnin Bata ke sauyawa. Ya shafe fiye da shekaru 30 a Equatorial Guinea, inda kakanninsa na wurin uwa suka fito. A yanzu haka ofishin raya al'adun Spain na bajakolin ayyukansa a birnin Bata.
  • Mutum na sanya kifi a kan wata mota
    Bangaran da gwamnati ke son bunkasa wa nan gaba shi ne noma. Kasar na da albarkatu da dama musamman na ruwa, sai dai yawancin abincin da suke ci ana shigowa da shi ne daga kasashen waje. Harkokin sufuri na kara bunkasa sakamakon kyawawan hanyoyi da ake ginawa.

BBC © 2012 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.